ABNA24 : Majiyar muryar JMI ta bayyana cewa manya –manyan jami’an sojojin kasar sun halarci wannan bikin akwai Janar Mohammad Bakiri babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran.
Makran yana da nauyin ton 121, sannan yana da tsawon mita 228, fadin mita 42 sannan zurfin mita 21.5.
Banda haka jirgin yana da wuraren saukar jiragen sama masu saukar ungulu har hudu, yana da kayakin aikin soje na zamani, da bindigigi masu sarrafa kansa, da kuma cilla makamai masu linzami daban-daban, har’ila yau zai iya samfani da kanan kwale-kwale da jiragen sama wadanda ake sarrafasu daga nesa.
Aikin jirgin ruwan yakin Makran shi ne yin sintiri da kuma raka jiragen ruwa a cikin tekn Indiya zuwa mashigar Babul Mandan na kasar Yemen, da kuma Tekun maliya.
342/