3 Janairu 2021 - 10:01
Nijar : Jam’iyya Mai Mulki Ce Ke Da Rinjaye A Majalisar Dokoki

Jam’iyyar PNDS tarraya mai mulki a Jamhuriyar NIjar, ta samu gagarimin rinjaye a majalisar dokokin kasar, bayan lashe zaben shugaban kasar da za’a je zagayensa na biyu da tazara mai yawa.

ABNA24 : PNDS, ta samu kujera 80 daga cikin 166, yayin da jam’iyyar Moden Lumana ta samu 19, sai kuma MNSD-nassara da MPR Jamhuriya suka samu guda 13 ko wannensu.

Saidai wasu jam’iyyun sun ce zasu shigar da korafi saboda zargin magudi da aikata ba daidai ba a zaben da aka gudanar a ranar 27 ga watan Disamba da ya gabata.

A jiya ne Hukumar zabe ta kasa a jamhuriyar Nijar, ta sanar da sakamakon wucin gadi na zaben shugaban kasar da aka kada kuri’arsa a ranar 27 ga watan Disamba da ya gabata.

Sakamakon da hukumar ta fitar a safiyar wannan Asabar ya nuna cewa dan takarar jam’iyyar PNDS-Tarrayya mai mulki ne cewa da Malam Bazoum Mohamed, ne kan gaba, da kashi 39,33 cikin dari, kwatankwacin kuri’in kimanin miliyan 1,9 yayin da tsohon shugaba Alhaji Mahamane Usman , na jam’iyyar RDR Canji ne ke biye masa da kashi 16,99 cikin dari na yawan kuri’un da aka kada.

Hakan dai yana nufin za’a je zagaye na biyu a zaben shugabancin kasar a karshen watan Fabrairu mai zuwa, tsakanin Bazoum Mohamed da Mahamane Usman.

342/