23 Disamba 2020 - 14:34
Najeriya : Kungiyar ASUU Ta Janye Yajin Aiki

Kungiyar malaman jami'o'i ta Najeriya cewa da ASUU ta janye yajin aikin data kwashe kusan wata tara tana yi.

ABNA24 : Rahotanni daga Najeriyar sun ce an cimma yarjejeniya tsakanin gwamnati da kungiyar bayan shafe sa'o’i takwas suna tattaunawar sirri a Abuja.

Yayin tattaunawar gwamnati ta amince biyan malaman jami’o’in naira biliyan arba’in na alawus da kuma wasu naira biliyan talatin na gyare-gyaren jami'o'i.

Yajin aikin da malaman jami’o’in na Najeriya suka kwashe wata tara sunayi ya dai jefa daliban jami’o’in kasar cikin halin ni ‘yasu.

342/