ABNA24 : Kwamitin shugaban kasar ne da ke yaki da annobar korona, ya bukaci ma'aikatan gwamnati daga mataki na 12 zuwa kasa da su zauna a gida har na tsawon makonni biyar.
Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya ce za’a rufe duka makarantu a fadin kasar har zuwa watan Janairun shekara ta 2021 mai shirin kamawa.
Haka kuma gidajen rawa da wuraren motsa jiki za su ci gaba da zama a rufe a kasar, kamar yadda kuma za’a rufe gidajen cin abinci.
A game da wuraren ibada kuwa gwamnatin ta bukaci ko wanne wuri kada a wuce kasha 50 cikin 100 na mutanen da yake dauka a baya.
A Najeriya dai kawo yanzu mutane 78,790 ne aka tabbatar sun kamu da cutar korona, bayan gano wasu 356 da suka harbu da cikin sa’o’I 24 da suka gabata, yayin da kuma adadin wadanda cutar ta kashe tun bayan bullarta ya kai 1,227 a cewar hukumar dakile yaduwar cutuka ta kasar NCDC.
342/