8 Disamba 2020 - 11:55
Ana Ci Gaba Da Samun Koma Bayan Masu Mutuwar Daga Cutar Corona A Iran

Kakakin ma’aikatar kiwon lafiya ta Iran Sima Sadat Lari, a taron manema labaru da take yi a kowace rana, ta sanar a yau Litinin cewa; A cikin sa’oi 24 da su ka gabata adadin wadanda cutar ta corona ta kashe su ne; 284, da hakan yake nuni da samun koma baya matuka na masu rasa rayukansu.

ABNA24 : Daga bullar cutar corona zuwa yanzu dai ta kashe mutanen da suka kai 50, da 594.

Har ila yau, a cikin wannan tsakanin mutanen da su ka kamu da cutar su ne dubu 10 da 827. Wadanda suke a kwance a gadajen asibiti kuwa sun kai 691.

A makwanni kadan da su ka gabata adadin masu kamuwa da cutar da kuma wadanda ake kwantarwa a gado sun fi haka yawa.

342/