ABNA24 : Shugaban kasar ta Ghna Addo Dankwa Akufo-Addo ya jaddada azamarsa ta ganin an gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali, sannan kuma zai karbi sakamakon zaben a duk yadda ya zo.
A jiya juma’a ne dai shugaban kasar na Ghana ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da jawabi akan cimma yarjejeniyar zaman lafiya ta 2020 wacce aka yi a Hotel din Movenpick a birnin Accra.
A ranar Litinin mai zuwa ne dai za a yi zaben shugaban kasa a kasar Ghana.
342/