5 Disamba 2020 - 10:29
​Rasha Ta Soki Hukumar IAEA Saboda Fitar Da Wasu Bayanan Sirri Na Kasar Iran

Gwamnatin kasar Rasha ta soki hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya saboda fitar da wasu bayanan sirri na kasar Iran.

ABNA24 : Jakadan Rasha a ofishin majalisar dinkin duniya a birnin Viena na kasar Austria Mikhail Alyanov ya bayyana cewa, hukumar IAEA ta fitar da wasu bayanai na sirri da Iran ta aike mata, tun kafin manyan jami’an hukumar su samu bayanan.

Ya ce wasu kafofin yada labaran turai sun bayar da rahoto kan bayanan da kasar Iran ta aike wa hukumar, alhali manyan alkalan hukumar ba su da bayani kan hakan, sai da suka fara jin bayanan a kafofin yada labarai.

Jakadan na Rasha ya ce irin wannan mataki yana karya gwiwa matuka dangane da batun bayanai na sirri da ke tsakanin gwamnatoci da kuma babbar hukuma ta duniya ta nukiliya, wadda ayyukanta sun ginu a kan kiyaye sirrin kasashe.

Shi ma a nasa bangaren jakadan kasar ta Iran aofishin majlaisar dinkin dinkin duniya da ke Vienna, ya bayyanaabin da ya faru da cewa, hakan babban abin kunya ne ga wannan hukuma, kamar yadda kuma ya bukaci hukumar ta IAEA da ta dauki matakai na tabbatar da kiyaye sirrin dukkanin kasashe mambobinta.

342/