4 Disamba 2020 - 17:08
Nijar : ‘Yan Takara 359 Zasu Fafata A Zaben ‘Yan majalisar Dokoki

Kotun tsarin mulki a jamhuriyar Nijar, ta fitar da jerin sunayen ‘yan takaran da suka cancanci tsayawa takara a zaben ‘yan majalisar dokokin kasar.

ABNA24 : Daga cikin takardu 505 da kotun ta tantance, ban da na kasashen ketare, kotun ta amince da takardu 359, yayin data yi watsi da takarar mutum 146.

Wannan dai ya sanya ‘yan takara 359 ne zasu fafata domin samun wakilci a zauren majalisar dokokin kasar mai kujeru 171.

A ranar 27 ga watan Disamban nan ne za’a gudanar da zaben shugaban kasa zagayen farko gami dana ‘yan majalisar dokoki a kasar ta Nijar, yayin da kuma za;a gudanar da zaben kananan hukumomi a ranar 13 ga watan Disamban nan idan Allah ya kai.

342/