2 Disamba 2020 - 13:36
Iran: A Kowace Rana Ta Allah Karfinmu Na SojaYana Karuwa

Daya daga cikin manyan jami’an sojan kasar ta Iran janar Shirazy wanda ya gabatar da jawabi a wurin baje kolin kayan yaki na sojojin ruwan Iran ya ce; Sabbin kayan aiki na sadarwa da sojojin ruwa su ke amfani da su yana nuni ne da yadda sojojin na Iran su ke kara samun karfi.”

ABNA24 : Janar Shirazi ya kuma jaddada cewa sojojin ruwan na Iran da jiragen yaki a cikin yankuna masu nisa da hakan yake nuni da karfin da sojojin ruwan na jamhuriyar musulunci suke da shi.

Daga cikin yankunan da soja da kuma dakarun kare juyin musulunci na Iran su ked a jiragen yaki da akwai tekun India da kuwa wasu tekunan a kokarin da suke yi na kare al’umma da kasar Iran.

A yayin baje kolin da aka bude a jiya, an nuna sabbin kere-kere na kayan yaki da sojojin ruwan Iran suke amfani da su.

342/