ABNA24 : A lokacin da yake zantawa da manema labarai a yammacin jiya a birnin Tehran, kakakin hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasar Iran Behrouz Kamalvandi ya bayyana cewa, kwamitin kula da harkokin nukiliya na majalisar dokokin kasar ya gudanar da wani zama a jiya Talata, tare da halartar manyan jami’ai na hukumar kula da makamshin nukiliya ta Iran.
Ya ce a yayin tattaunawar, mambobin kwamitin sun bukaci jin ta bakin jami’an hukumar, kan yiwuwar yin amfani da wasu hanyoyi a karkashin hukumar, domin daikile tasirin takunkumin Amurka, daga ciki kuwa har da yiwuwar kara yawan sanadarin uranium da Iran din take tacewa a cibiyoyinta na nukiliya.
Kamalvandi ya ce, sun sheda wa kwamitin cewa hukumar ba ta da wata matsala a kan haka, a kowane lokaci aka cimma matsaya a tsakanin bangarorin da suke daukar matsaya a kan wadannan batutuwa, cibiyoyin nukiliya na kasar Iran za su iya kara yawan sanadarin uranium da suke tacewa.
Iran dai ta dauki matakin jingine yin aiki da wasu bangarori na yarjejeniyar nukiliya, sakamakon fitar da Amurka da Donald Trump ya yi daga wannan yarjejeniya, kamar yadda kuma kasashen turai suka kasa cika nasu alkawullan da suka dauka a kan wannan batu.
342/