ABNA24 : Ministan harkokin wajen na kasar Faransa Jean Y-Yves Le Darian yana son sama wa kasarsa mafita daga matsalar da ta jefa kanta a ciki na cin zarafin ma’akin Allah, annabi Muhammadu ( S.A.W.).
Bayan ganawa da ya yi da shugaban kasar Masar, Abdel Fattah al-Sisi, da takwaransa Sameh Shukri, ya kuma gana da shugaban cibiyar Azhar, Sheikh Ahmad al-Tayyib.
Ministan harkokin wajen na Faransa ya fadawa shugaban cibiyar ta Azhar cewa; Kasarsa tana matukar girmama addin musulunci.
Sake buga zanen cin zarafi ga addinin musulunci da kuma kiran da shugaban kasar Faransa Macron ya yi na cewa; Dole a yi wa addinin musulunci kwaskwarima sun jefa kasar cikin sa-in-sa da duniyar musulmi, inda ake yin kiraye-kirayena a kauracewa kayan da Faransan take kerawa.
342/