8 Nuwamba 2020 - 12:09
An Kaddamar Da Wani Sabon Kamfain Na Nuna Rashin Amincewa Da Kulla Alaka Da Isra’ila A Sudan

Kwamitin kula da gwagwarmayar nuna rashin amincewa da kulla alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila a Sudan ya sanar da bullo da wani sabon kamfain don sake nuna rashin amincewar al’ummar kasar da wannan shiri da gwamnatin kasar take da shi.

ABNA24 : Kwamitin ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar inda ya ce: Kamfain din zai kunshi taken rashin amincewa guda uku ne, wato: Rashin amincewa da shirin zaman lafiya da Isra’ila, rashin amincewa da tattaunawa da kulla yarjejeniya da Isra’ila da kuma rashin amincewa da yarda da haramtacciyar gwamnatin sahyoniyawa.

Sanarwar ta kara da cewa yayin wannan kamfain din ana fatan samun sanya hannun mutane alal akalla miliyan guda wadanda za su nuna rashin amincewarsu da kulla alaka ta diplomasiyya tsakanin Sudan da haramtacciyar kasar Isra’ila.

A kwanakin baya ne dai gwamnatin Amurka ta sanar da cewa gwamnatin Sudan ta shigo cikin sahun kasashen UAE da Bahrain wadanda suka sanya hannu kan yarjejeniyar kulla alaka da haramtacciyar kasar Isra’ilan, lamarin da ke ci gaba da fuskantar tofin Allah tsine daga bangarori daban-daban na ciki da wajen kasar ta Sudan.

Har ya zuwa yanzu dai ana ci gaba da samun taro da kuma gangamin jama’a a bangarori daban-daban na Sudan din da suke bukatar sabuwar gwamnatin kasar da ta dawo daga wannan kuduri nata na kulla alaka da Isra’ilan.

342/