ABNA24 : Obama ya kara da cewa shugaban yana son a fadi sunansa kawai inda aka yi maganar ci gaban tattalin arziki, amma baya son a ambace shi idan an yi maganar sakacin da ya yi a yaki da cutar korona har da kashe Amurka fiye da 220,000.
Har’ila yau Obama ya aibata shugaban dangane da yadda yake mu’amala da yan jiridu da kuma kafafen yada labarai a cikin shekaru 4 da suka gabata.
A jibi talata ce ake saran za’a gudanar da zaben shugaban kasa a kasar Amurka, wanda yake daga cikin zabubbuka masu zafi a tarihin kasar.(19)
342/