ABNA24 : Majiyar muryar jumhuriyar Musulunci ta Iran (JMI) ta nakalto majiyar ma’aikatar harkokin wajen kasar ta na cewa Zarif ya mika wannan ta’aziyyarce a cikin wani sakon da ya aikewa tokwaransa na kasar Turkiya Mevlut Cavusoglu.
Ministan ya kara da cewa JMI a shirye take ta tallafawa wadanda suka ji rauni ko suka cutu saboda girgizan kasar.
A jiya jumma’a ce girgizan kasa mai karfin ma’aunin richter 6.6 ta aukawa yankin Seferihisar da birnin Izmir a cikin lardin Izmir na kasar Turkiya wanda ya yi sandiyyar mutuwar mutane 4 da kuma raunata wasu 150.
342/