Gidan talabijin din na Akhbariyya ya watsa rahoton cewa: Sojojin gwamnatin Siriya sun fafata da wasu gungun 'yan ta'adda a kudancin garin Halab a safiyar yau Lahadi inda suka kashe da dama daga cikin 'yan ta'adda tare da tarwatsa motocin yakinsu.
Har ila yau jiragen saman yakin sojin Siriya sun yi luguden wuta kan tawagar motocin yakin 'yan ta'adda a yankunan arewacin garin na Halab inda suka kashe matuka motocin tare da jikkata wasu na daban.288