Rahoton da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar na cewa a cikin watanni shida da suka gabata, kungiyar ta fadada ayyukanta zuwa cikin kasashe 11 inda ta kashe akalla mutane 500 dukkaninsu fararen hula.
Rahoton ya ambaci sunayen kasashen da lamarin ya shafa da suka hada da Bangladesh da Belgium da Masar da Faransa da kuma Jamus da Indonesia, Lebanon da Pakistan da Rasha da Turkiyya da kuma Amurka.
Hare-haren da ta kai a wadannan kasashe, na kara tabbatar da cewa kungiyar na fatan ganin ayyukanta sun gama duniya, kuma fararen hula ne suka fi kasancewa a cikin hatsari.
Wani abin fargaba da kungiyar ke haifarwa a duniya a cewar rahoton, shi ne yadda da dama daga cikin mayakanta suka fice daga Syria da kuma Iraqi sakamakon hare-haren da suke fuskanta, inda a yanzu suke sheke ayarsu a cikin kasar Libya.288