Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewar a wata sanarwa da mahukuntan Nijeriyan suka fitar a jiya Litinin an bayyana cewar a ranar Alhamis mai zuwa ne shugaba Buharin zai kai ziyarar don kaddamar da shirin tsarkake yankin daga matsalar gurbatar yanayi da yake fuskanta don magance wa mutanen yankin daya daga cikin manyan matsalolin da ke damunsu.
A ranar Lahadin da ta gabata ne dai, shugaba Buharin ya sanar da cewa gwamnatinsa za ta tattauna da shugabannin yankin Niger Deltan don samo hanyar da za a magance musu matsaloli da korafe-korafen da suke da su.
Ziyarar ta shugaba Buhari ta zo ne a daidai lokacin lokacin da sabuwar kungiyar tsagerun yankin Niger Delta mai suna Niger Delta Avengers (NDA) suke ci gaba da kai hare-hare kan bututun man fetur da kuma kayayyakin kamfanonin da suke hako mai din a yankin lamarin da ke ci gaba da zagon kasa ga tattalin arzikin kasar.288