11 Mayu 2016 - 15:07
Harin Ta'addanci Ya Lashe Rayukan Mutane a Iraki

Wata mota da aka makare da bama-bamai ta tarwatse a unguwar Sadar da ke gefen birnin Bagadaza fadar mulkin kasar Iraki, inda ta lashe rayukan mutane kimanin 30 tare da jikkata wasu fiye da 40 na daban.

Majiyar rundunar 'yan sandan Iraki ta sanar da cewa: Wata mota da aka makare da bama-bamai ta tarwatse a cikin kasuwar Unguwar Sadar da ke gefen birnin Bagadaza fadar mulkin kasar Iraki a safiyar yau Laraba, inda ta janyo mutuwar mutane akalla 28 tare da jikkatan wasu fiye da 40 na daban.

Jami'an tsaron gwamnatin Iraki ta killace wajen da aka kai harin tare da jigilar mutanen da suka samu raunuka zuwa asibiti domin jinya.

Har ila yau jami'an tsaron Iraki sun kai samame yankin Al-Boukhamis da ke arewacin birnin Bagadaza, inda suka ritsa da 'yan ta'addan da suke kai hare-haren ta'addanci, amma 'yan ta'addan hudu sun tarwatsa kansu a cikin motar da suka makare da bama-bamai, kuma babu wani jami'in tsaro da ya samu rauni.288