21 Afirilu 2016 - 17:07
Boko Haram na ba Matasa tallafi

Rundunar Sojin Najeriya tace ta gano cewa Mayakan Boko Haram na janyo hankalin matasa wajen ba su tallafi domin shiga kungiyar ta hanyar rancen kudi musamman ‘yan kasuwa a yankin arewa maso gabashi mai fama da hare-haren kungiyar.

Hedikwatar tsaro a Najeriya tace kungiyar na yin haka ne sakamakon luguden wutar da dakarun Najeriya ke yi wa mabuyar mayakanta.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin ma’aikatar tsaron Janar Rabe Abubakar ta ce tuni kungiyar Boko Haram ke daukar Matasa ta hanyar ba su rancen kudi a yankin arewa maso gabashi.

Sanarwar tace kungiyar na janyo hankalin masu kananan sana’oi kamar masu sana’ar dinki da mahauta da wasu sana’oin hannu.

Sanarwar tace bayan karbar bashin ana ba mutanen zabi ko dai su shiga kungiyar ko kuma a kashe su idan sun kasa biyan bashin a wa’adin da aka ba su.

Ma’aikatar tsaron ta Najeriya ta bukaci al’umma musamman a yankin arewa maso gabashi su yi takatsantsan da dubarun da ‘Yan Boko Haram ke bi na kokarin sun samu sabbin mabiya bayan an tarwatsa su.

Sannan sanarwar ta gargadi mutane su kaucewa karbar rance daga hannun wadanda hukuma ba ta san da zamansu ba.288