Wannan janyewar da jam'iyyun adawar suka yi, kenan za ta ba wa shugaba Muhammadou Issoufou cinye zagaye na biyu na zaben shugaban kasar.
Tun a watan Nuwamban bara ne ake tsare da Hama Amadou a gidan-kaso, sakamakon zargin da ake masa na fataucin jarirai, amma ya musanta, yana cewa bi-ta-da-kulli ce ta siyasa.
A zagayen farko na zaben dai, shugaba Muhammadou Issoufou ya samu sama da kashi 48 bisa dari na kuri'un da aka kada, inda ya rage kiris da ya samu adadin kuri'un da za su ba shi rinjaye a zaben.288