Hakan ya biyo bayan wani rikici da ake zargi tsakanin 'Yarbawa - Area Boys da kuma 'yan asalin arewacin kasar.
Rikicin dai ya yi ta ruruwa ne tun daga ranar Talata tsakanin area boys din da kuma 'yan Okada.
Yanzu haka dai an tura jami'an tsaro domin kwantar da lamarin.
Rikicin kabila wani al'amari ne da yake addabar sassa daban-daban na Najeriya.288