A hirar da ya yi da kamfanin dillancin labaran Faransa AFP, shugaba al-Assad ya bayyana cewa mawuyaci ne a kawo karshen rikicin kasar cikin kankanin lokaci, yayin da kasashen duniya ke fatan ganin an aiwatar da yarjejeniyar tsagawaita wuta a kasar ta Syria nanda mako guda.
Shugaban ya kara da cewa, babban makasudin farmakin da dakarun gwamnatinsa suka kai lardin Aleppo, shi ne katse hanyoyin da ‘yan tawayen ke samun tallafi daga Turkiya.288