Firayi ministan kasar Rashan ya bayyana hakan ne a hirar da yayi da wata jaridar kasar Jamus (Handelsblatt) inda ya ce abin da ya kamata shi ne dukkanin kasashen da suke da bakin magana cikin rikicin Siriya su zauna teburin tattaunawa don kawo karshen rikicin Siriya maimakon yin abin da zai haifar da sabon yakin duniya.
Don haka sai Firayi minista Medvedev ya kirayi Amurka da kawayenta na kasashen larabawa da cewa su sake tunani kan wannan lamarin in dai ba suna son haifar da yakin da ba shi da lokacin karewa ba ne.
A kwanakin baya ne dai kasar Saudiyya ta sanar da aniyarta na turawa da sojoji zuwa kasar Siriya da sunan fada da kungiyar Da'esh, lamarin da Amurka ta yi na'am da shi amma gwamnatin kasar Siriyan ta yi watsi da shi tana mai jan kunnen Saudiyya da kada ma ta fara tunanin haka, don kuwa Siriyan za ta mayar da kakkausar martani ga hakan.288