25 Janairu 2016 - 16:11
An Tsaurara Matakan Tsaro A Masar

Jami'an Tsaron Masar Sun Tsaurara Matakan Tsaro A Duk Fadin Kasar

Ma'aikatar harkokin cikin gidan Masar ta sanar da tsaurara matakan tsaro a duk fadin kasar domin tsoron bullar rikici a yayin bikin tunawa da fara boren al'ummar Masar da ya kawo karshen mulkin kama karyar Hosni Mubarak a shekara ta 2011.

Ma'aikatar harkokin cikin gidan Masar ta sanar da cewa ta jibge rundunar tsaro a sassa daban daban na kasar domin tabbatar da tsaro da oda a daidai lokacin da al'ummar Masar ke gudanar da bukukuwan cika shekaru biyar cur da boren da ya kawo karshen mulkin kama karyar shugaban Hosni Mubarak da ya shafe tsawon shekaru kimanin 30 yana mulki.

A ranar 25 ga watan Janairun shekara ta 2011 ne al'ummar Masar suka fara gudanar da boren nuna kin amincewa da mulkin kama karyar shugaba Husni Mubarak, inda boren ya kai ga faduwar gwamnatinsa a ranar 11 ga watan Fabrairun shekara ta 2011, don haka al'ummar Masar ke gudanar da bikin tunawa da wannan gagarumar nasara a yau.288