17 Janairu 2016 - 11:46
An cire wa Iran takunkumi

Shugaba Hassan Rouhani yace dage takunkumin da aka kakabawa kasarsa, ya bude sabuwar hanyar alaka tsakanin Iran da kasashen duniya.

Shugaban kasar Iran ya gabatar da murnarsa ga al’ummar Iran kan gagarumar nasarar da suka samu a fagen takaddamar shirin Iran na makamashin nukiliya.

A bayan sanar da dage takunkumin da aka kakaba wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan shirinta na makamashin nukiliya a jiya Asabar: Shugaban kasar Iran Dr Hasan Ruhani ya fitar da sakon taya al’ummar Iran murnar samun wannan gagarumar nasara mai daraja yana mai jaddada godiyarsa ga Allah Madaukaki kan gagarumar nasarar da ya bai wa kasar Iran a fagen takaddamarta da manyan kasashen duniya.

Tun a yammacin jiya Asabar ce a taron manema labarai da suka gudanar a birnin Viena; Ministan harkokin wajen kungiyar tarayyar Turai Federica Mogherini da takwararta na kasar Iran Muhammad Jawad Zarif suka sanar da cewa; Kungiyoyin kasa da kasa sun dage takunkumin da suka kakaba kan kasar Iran dangane da shirinta na makamashin nukiliya sakamakon yarjejeniyar da suka cimma tun a ranar 14 ga watan Yulin shekarar da ta gabata ta 2015.

A nata bangaren kungiyar tarayyar Turai a yammacin jiya Asabar ta sanar da dage dukkanin takunkumin tattalin arziki da na kudade da ta kakaba kan kasar Iran. Kamar yadda a yammacin jiyan sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry ya sanar da cewa; Amurka ta dage takunkumin da ta kakaba kan kasar Iran sakamakon yarjejeniyar da aka cimma kan shirin Iran na makamashin nukiliya tun a watan Yulin shekarar da ta gabata tsakanin Iran da manyan kasashen duniya.288