16 Janairu 2016 - 12:03

Hukumomi a Burkina Faso sun ce mutane 22 ne suka mutu a wani hari da wasu 'yan bindiga suka kai wani otal Ouagadougou, babban birnin kasar.

Ministan harkokin cikin gida Simon Compaore ya ce tuni aka kawo karshen kawanyar da maharan suka yi wa otal din Splendide, amma ana ci gaba da gumurzu da su a wani otal da ke kusa da shi.

Ministan ya ce an kashe uku daga cikin maharan, yayin da aka tserar da mutane kimanin 126 daga cikin otal din, wanda yawanci Turawa ke sauka288