15 Janairu 2016 - 12:39
An Karfafa Matakan Tsaro Bayan Harin Jakarta

yan Sanda a Indonusiya na cikin shirin ko ta kwana a washe garin harin ta'adancin Jakarta daya girgiza kasar.

Masu bincike a wannan kasa mafi yawan musulmi a Duniya na zargin kungiyar IS dage yankin Asiya ta kudu maso gabas da shirya harin.

kawo yanzu dai hukumomin kasar sun sanar da cafke mutane hudu da ake zargi da hannu a hare-haren na jiyya da suka yi sanadin mutuwar mutane tara tareda maharan biyar, kana wasu 24 suka jikkata.

Kakakin 'yan sanda a wannan kasar ya tabbatar da cewa na tantance mahara hudu da suka kai harin kuma a binciken da ake ci gaba da yi an gano cewa suna da alaka da kungiyar IS.288