Wasu rahotannin ma na cewa ana zargin an kona gidan tsohon mataimakin gwamnan jihar wanda dan jam'iyyar PDP ne.
Sai dai mataimakin shugaban 'yan sanda DIG Salihu Hashimu ARgungu , wanda mai sa ido ne a zaben, ya shaida wa manema labarai cewa babu abin da ya faru kuma komai yana tafiya yadda aka tsara.
An dai fara zaben a kan lokaci a wasu rumfunan amma a wasu wuraren har zuwa karfe biyu na ranar Asabar ba a fara kada kuri'a ba.
Tun da fari Kakakin hukumar zabe ta kasa INEC, Mista Nick Dazan, ya yi wa wakilinmu bbc: karin bayani kan yadda hukumarsu ta shirya don zaben:288