25 Disamba 2015 - 13:04

Rahotanni daga Nijeriya, na nuni da cewa kimanin mutane dari (100) sun rasa rayukansu biyo bayan wata gobara da ta faru a wata masana'antar iskar gas a garin Nnewi, da ke jihar Anambra, da ke kudu maso gabashin Nijeriyan.

Rahotannin sun ce gobarar ta tashi ne lokacin da wata motar daukar iskar gas ke sauke kayan da take dauke da shi a tashar iskar gas din Chikason da ke garin na Nnewi mai tsohon tarihin, inda mutane da yawa suka kone ciki kuwa da ma'aikatan kamfanin da kuma mutanen da suka zo kamfanin don sayen iskar gas din saboda bukukuwan Kirsimeti.

Wani shaidan gani da ido ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Associated Press cewa lamarin ya faru ne bayan da motar daukar gas din ta gama sauke kayan da take dauke da shi amma ba ta jira ta tazarar da aka tsara na jira don ta huce ba, inda ta kama tafiya don haka motar ta yi bindiga.

Duk da cewa har ya zuwa yanzu hukumomi ba su tantance yawan mutanen da suka mutu ba amma kamfanin dillancin labaran Associated Press din ya ce dan rahotonsa ya shaida masa cewa ya ga gawawwakin mutane 100 da suka mutu.288