Kungiyar ta sanar ta radiyo cewa mabiyanta ne suka kai harin.
Sai dai kuma sanarwar ba ta nuna cewa 'yan kungiyar ta IS na da hannu wajen tsara kai harin ba.
Tunda farko hukumar tsaro ta FBI tace tana gudanar da bincike, a kan rahotannin dake nuna cewa matar mutumin Tashfin Malik, ta sha rantsuwar yin biyayya ga jagoran kungiyar mayakan IS ta hanyar shafin sada zumunta na Facebook.288