1 Nuwamba 2015 - 15:32
Rasha Da Jahar Bauchi Sun Rattaba Hannu Kan Hakar Mai Da Iskar Gas

A wani cigaba a kokarin da ake na samun mai a arewacin Najeriya, jahar Bauchi da wani kamfanin hako ma'adinai na kasar Rasha na shirin hako mai a Bauchin.

Gwamnatin jahar Bauchi da wani kamfanin hakar mai da ke kasar Rasha sun rattaba hannu kan wata yarjajjeniyar kasuwanci ta hako mai da iskar gas a jahar Bauchi. Wannan, a cewar wakilinmu a Bauchi Abdulwahab Muhammad, ya zo daidai na shelar da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi na  ba da himma wajen harkar hako albarkatun mai a arewacin Najeriya.

Hakazalika, gwamnan jahar Bauchi, Alhaji Mohammed Abdullahi Abubakar,  y ace za a rinka karbar haraji kan duk masu hakar ma’adinai a jahar, wanda don haka ne ma aka bullo da wata sabuwar doka. Y ace da zarar an kaddamar da dokar za a cigaba da karbar haraji da kuma harkokin hakar ma’adinai gadan-gadan.

Gwamnan na jahar Bauchi y ace kamfanin hakar ma’adinan na kasar Rasha na daya daga cikin kamfanonin da su ka shaharar a harkar ma’adinai a duniya, wanda ya tabbatar da kasancewar mai a arewacin Najeriya – musamman ma Bauchi. 289