A wata sanarwa da kakakin rundunar sojin kasa, Kanar Sani Usman Kukasheka ya fitar, ya ce mutanen da aka ceto sun hada da maza takwas da mata 138 da yara 192.
Ya kara da cewa an kai su garin Mubi da ke jihar Adamawa domin duba lafiyarsu.
Kanar Kukasheka ya ce dakarunsu sun kashe 'yan kungiyar boko Haram 30, sannan suka lalata manyan sansanoninsu a kauyuka hudu da ke kusa da dajin Sambisa.
Sanarwar ta kara da cewa sojojin sun kwato makamai daban-daban daga hannun 'yan kungiyar ta Boko Haram. 289