Mai Magana da yawun rundunar sojin kasar Kanar Sani Usman Kukasheka ya tabbatar da tashin bama-baman a Gomari da Ajilari.
To sai dai kawo yanzu babu wata kungiya da ta yi ikirarin kaddamar da wannan harin, sai dai hakan na zuwa ne bayan wata murya da shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya fitar, inda ya musanta cewa Sojin Najeriya na samun galaba kan mayakan na Boko Haram. 289