30 Agusta 2015 - 19:19

Daruruwan mutane suka taru a husayyniyar baqiyatullah domin daga tutar hubbaren Imam Ridha (as) da aka karrama shaikh zakzaki da ita a wata ziyara da ya kawo birnin Mashahad dake kasar Iran. shaikh zakzaki ya gudanar da jawabi bayan sanya tutuar inda ya yi nuni game da muhimmanci da kuma matsayin da wannan tuta take dashi.

An Gudanar da gagarumin buki a lokacin dora tututar Kubbar Imam Rihda (As) a hussainiyar baqiyyatullah dake birnin zaria a arewacin Nigeria.

Bukin da aka gudanar da shi wanda jagoran harkar musulunci a Nigeria shaikh Ibrahim Elzakaki ya samu halartar mutane masu yawa, inda ka gudanar da fareti kafin daga bisani aka daga tutar Haramin Imam Ridha wadda aka karrama shaikh zakzaki da ita a lokacin ziyarar da ya kawo birinin Mashahad na kasar Iran,

A cikin jawabinsa a lokacin bukin jagoran harkar musulunci a Nigeria ya bayyana irin mastayin da wannan tuta take da shi musamman idan aka yi la’akari da cewa tutace da aka dora ta akan kubbar hubbaren Imam Ridha (As) limami na 8 daga cikin jerin limaman shirya 12 na iyan gidan manzon All.. tsira da aminci su tabata gareshi da iyalan gidansa tsarkaka288