21 Agusta 2015 - 17:32

A cikin wannan watan da muke ciki ne za'a gudanar da taro kan batun samar da tsaro a tekun Guinea, manyan hafsoshin sojin sama guda 20 ne zasu halarci taron daga nahiyoyin Afrika, Turai da kuma Kasar Amurka, taron zai tattauna en game da batutuwan da suka shafi sabbin hanyoyin zamani na samar da tsaro ga yankin tekun Guinea.

Kimanin Hafsoshin sojin ruwa 20 daga kasashen Afrika da Turai da Amurka za su taru a Nigeria domin tattaunawa game da batun matsalar tsaro a tekun Guinea.

Dukan kasashen da abin ya shafa sun nuna aniyarsu ta halartar taron da za’a yi kan batun manfetur a bana wanda kwamnadan hafsan hafsoshin ruwa na Nigeria Vice Admiral IbokEkwe Ibas zai jagoranta.

Shugaban kwamitin gidnarwa na shirya taron Admiral Begro Ibe Enwo ya bayana cewa Daga cikin muhimman batutuwan da taron zai maida hankali akai akwai batun fada da yan fashin doron ruwa, da musayar kimiya da fasaha da kuma kera jiragen jirgin ruwa acikin gida da kuma baje kolin kayayakin da ake amfani da su wajen samar da tsaro ga cibiyoyin samar da Manfetur da iskar Gas.

Kuma ana saran gabatar da kasidu daban-daban da suka shafi harkar teku da samar da tsaro,da sauransu. Daga ranar 24 zuwa 26 ga watan Agusta da muke ciki288.