Mai magana da yawun ma’aikatar tsaron Amurka Kaftin Jeff Davis ya ce a ranar 8 ga wannan wata na Yuli ne suka kai harin, kuma daga bisani sun tabbatar da mutuwar Kwamandan da ke jagorantar kungiyar Khorasan, reshn kungiyar Al Qaeda.
Fadhli wanda aka ce dan asalin kasar Kuwait ne, yana cikin manyan kwamandojin shugaban Al Qaeda marigayi Osama bin laden.288