17 Yuli 2015 - 14:42
Ayatollah Khamenei: Dole Ne Jami'an Iran Su Yi Taka Tsatsan Matuka Dangane Da Yarjejeniyar Nukiliya

Jagoran juyin juya halin muslunci a Iran ya hannunka mai sanda ga jami’an gwamnatin kasar da su sanya lura matuka dangane da yarjejeniyar nukiliya da aka cimma, da kuma yadda daya bangaren yake yin aiki da ita

Jagoran ya bayyana hakan ne a cikin wata amsar wata wasika da shugaba Hassan Rauhani ya aike masa, inda ya bayyana cewa dole ne jami’an na Iran su zama cikin fadaka matuka dangane da wannan lamari, musamman ma ganin cewa wasu daga cikin manyan kasashen da aka cimma wannan yarjejeniya da su, ba abin amincewa ba ne ga Iran.

A cikin wasikar wadda shugaba Rauhani ya aike wa jagoran, ya yi masa bayani a jimlace kan yadda tattaunawar ta gudana, tare da mika godiya ga jagoran dangane da irin shawarwarin da ya rika bayarwa kan hakan, wanda hakan ne ya kai tattaunawar ga nasara.288