A ranar 3 ga watan Yuli ne Babban hafsan Sojin Masar wanda a yanzu shi ne shugaban kasa Abdel Fattah al Sisi ya hambarar da Morsi bayan shafe kwanaki ana zanga-zangar kin jinin gwamnatin ‘Yan uwa musulmi.
Tun lokacin ne kuma mahukunatan Masar karkashin jagorancin Morsi ke kamewa tare da kashe magoya bayan Morsi.
An kashe daruruwan mutane tare da kame dubbai da yanke wa daruruwa hukuncin kisa.
Morsi na cikin wadanda aka yanke wa hukuncin kisa tare da wasu manyan shugabannin Jam’iyyar ‘Yan uwa Musulmi.
Yanzu haka kuma Masar na ci gaba da fuskantar hare hare daga Mayakan IS a yankin Sinai inda aka hallaka rayukan mutane da dama.288