24 Yuni 2015 - 12:58
Boko Haram ta kashe mutane 42 a Debiro Biu da Hawul

‘Yan Sandan jihar Borno sun tabbatar da mutuwar akalla mutane 42 wadanda wasu 'Yan bindiga da ake tunanin Mayakan Boko Haram ne suka harbe har lahira bayan sun kaddamar da hari a Biu da Hawul da ke cikin Jihar Borno a Najeriya.

Mazauna yankin sun ce Maharan sun shigo kauyukan Debiro Hawul da Debiro Biu ne a saman Babur da mota a kori kura a ranar Litinin inda suka bude wuta tare da kona gidaje da wawure dukiyoyin jama’a.

Hare hare nan zuwa ne a yayin da al’ummar da ke Arewa maso Gabashin Najeriya ke cigaba da bayyana damuwar akan yawan hare haren da ake kai wa a Yankin.

A cikin kwanaki biyu da suka gabata, an kai irin wadannan munanan hare hare sau biyu a Gujba da Maiduguri inda aka samu rasa rayukan mutane kusan 30.

Rahotanni kuma sun ce yara mata ke kai harin abin da ke dada jefa tsoro cikin al’umma a dai dai lokacin da gwamnati ke kokarin murkushe Mayakan Boko Haram.288