Kasashen dai sun hada da Najeriya da Kamaru da Chadi da Jamhuriyar Nijar da Benin.
Wannan taro dai na zuwa ne bayan tarukan da manyan hafsoshin sojin kasashen suka yi ranar Talata da wanda ministocin tsaronsu suka yi ranar Laraba, inda suka shata wasu manufofi na tabbatar da nasarar yaki da ta'addanci.
Tuni dai shugabannin suka umarci Hukumar Raya Tafkin Chadi ta bullo da wani shiri na samar wa matasa ayyukan yi da nufin taimakawa wajen rage talauci a yankin arewa maso gabashin Najeriya da kuma sauran yankunan da tashe-tashen hankula na mayakan kungiyar Boko Haram suka lalata.288