31 Mayu 2015 - 10:30
Zabe: Erdogan ya nemi goyon bayan Musulmai

Shugaban Turkiya, Rajap Tayyib Erdogan ya nemi goyon bayan musulmai masu ra'ayin mazan jiya a zaben 'yan majalisar dokokin kasar da za a gudanar nan da mako guda.

A wani jawabi daya gabatar na bukin tunawa da ranar kafa daular Othomaniya, Mista Erdogan ya sanya lamarin addini a gaba gaba, yana mai tabbatar wa Musulmai cewa za a ci gaba da kiran sallah a kasar a fili.

Ya ce jam'iyyar ta sa AK wadda take da asali da addinin Musulunci, ba zata bi ra'ayin masu adawa da ci gaba da tasirin kafuwar daular Othomaniya tun a shekarar 1453.

Abokan hamayyar sa na ganin shawo kan masu ra'ayin 'yan mazan jiya da suka hada da Kurdawa akan su marawa jam'iyyar sa baya barazana ce ga demukradiyya.

Shugaban Turkiya na farko, Mustafa Kemal Ataturk shi ya soke aiki da tsarin musulunci a 1934, sannan ya daukaka al'adun turawa da suka hada da sanya tufafi da bai wa mata 'yanci.

Sai dai karfafa sha'anin addinin musulunci da Mista Erdogan ya yi, ya farfado da addinin a kasar.ABNA