5 Mayu 2025 - 10:51
Source: ABNA24
Fursunonin Gidan Yarin Hillah Na Lardin Babil Sun Tsere, Ana Ci Gaba Da Bincike A Kansu

Iraki ta bayar da sanarwar tserewar fursunoni daga gidan yarin Hillah na lardin Babil, tare nemansu ruwa a jallo

Wata majiyar tsaro ta rawaito cewa fursunonin sun tsere daga gidan gyaran hali na Hilla da ke gundumar Babil a kudancin Bagadaza babban birnin kasar, kuma ana ci gaba da neman su.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa Ahlul Bayt (as) - ABNA - ya habarta cewa: majiyar ta bayyana cewa jami’an tsaro a kasar Irak lardin Babila na ci gaba da gudanar da wani bincike na neman mutanen biyu da suka tsere. Majiyar ta bayyana cewa " fursunoni biyu sun tsere daga tsohuwar gidan gyaran hali na Hillah da ke karamar hukumar Babil". Ya kara da cewa "Jami'an tsaro a lardin sun kaddamar da wani sumame na nemansu a yankin". Wannan dai ba shi ne karon farko da fursunoni ke tserewa ba. A cikin 'yan shekarun nan, fursunonin sun tsere saboda dalilai daban-daban, ciki har da cin hanci da rashawa da hada baki da wadanda suka gudu.

Your Comment

You are replying to: .
captcha