4 Mayu 2025 - 11:17
Source: ABNA24
Yamen Ta Kai Hari Ga Filin Jirgin Ben Gurion Na Isra'ila+ Bidiyo 

Majiyoyi na yaren Hebrew sun ba da rahoton cewa an yi ta jin karar ƙararrawa a Tel Aviv, biyo bayan harin da Yamen ta kai kan filin jirgin Ben Gurion.

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As -Abna- ya habarta cewa: matsugunan Kudus da Yammacin Kogin Jordan saboda makami suna shan ruwan makamai masu daga Yemen. Inda Kafofin yada labaran suka bayar da rahoton cewa, an ji karar fashewar wasu abubuwa da dama a kusa da filin jirgin na Ben Gurion.

Bayan faruwar lamarin, an dakatar da zirga-zirgar jiragen sama daga filin jirgin sama na Ben Gurion.

Jaridar "Isra'ila Today" ta harshen Hebrew ta bayar da rahoton cewa, an harba makami mai linzami daga Yaman zuwa Palasdinu da aka mamaye.

Kuma na'urorin kariyat tsaro na Hitz da THAAD sun gaza wajen tinkarar makami mai linzami na Yaman

Tashar talabijin ta 12 ta Isra'ila ta sanar da cewa, bisa alkalumman da jami'an tsaro suka bayar, na'urorin Hitz da THAAD sun gaza yin gaba da gaba da makamin da aka harba daga Yemen.

Biyo bayan harin daruruwan yahudawan sahyoniya sun tsere zuwa matsuguni saboda fargabar makamin na Yaman

Jaridar "Isra'ila Today" ta harshen Hebrew ta bayar da rahoton cewa, daruruwan sahyoniyawan 'yan kaka gida sun gudu zuwa matsuguni, bayan da aka harba makami mai linzami daga Yaman zuwa Palastinu da aka mamaye, wanda ya afka kusa da filin jirgin sama na Ben Gurion.

Dakarun tsaron sararin samaniyar sojojin Isra'ila sun kasa dakile makamin na Yaman

Almog Booker, wakilin tashar talbijin ta 13 ta Isra'ila, ya bayar da rahoton cewa, na'urorin tsaron sararin samaniyar sojojin gwamnatin kasar sun gaza dakile makamin da aka harba daga kasar Yemen.

Your Comment

You are replying to: .
captcha