Kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta fitar da sanarwar cewa:
Hizbullah ta yaba da matakin da bai misaltuwa na sojojin Yaman da suka kai hari a filin tashi da saukar jiragen sama na Ben Gurion da ke cibiyar gwamnatin sahyoniyawa, tare da ketare duk wani tsarin tsaro na yahudawan sahyoniya da Amurka, ya kai ga cimma hadafin da madaidaici da aka nufa tare kuma da wargaza duk wani kwarjini na wannan gwamnatin.
Wannan harin na jarumtaka ya sake tabbatar da ƙasa agwiwar wuce gona da irin da Amurka da Birtaniyya suke yi a kan kasar Yamen da kuma gazawarta wajen karya ikon al'ummar kasar Yemen ko tilasta musu ja da baya daga matsayi mai daraja na goyon bayan Gaza, da kawar da kawayanyar da akai ma ta, da gaba da gaba ga yakin da makiya yahudawan sahyoniya suke yi da fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba.
Mataki tsayayye kai tsaye na al'ummar kasar Yemen masu daraja da hikima da jajircewa wajen nuna goyon baya ga Gaza da al'ummarta masu tsayin daka, duk kuwa da ci gaba da wuce gona da iri da kawanyar zalunci da aka yi mata, abin alfahari ne ga dukkanin al'ummar kasar masu 'yanci. Wannan hujja ce ga dukkan kasashen Larabawa da kasashen musulmi, kuma bisa kawar da kai da yanayin da ta ke ci ki ta wajabta wa kowa, ko da wane irin yanayi, ya yi amfani da dukkan karfinsa wajen tallafa wa Gaza da al'ummarta.
Kwamitin gwagwarmayar Falasdinu sun fitar da sanarwar cewa:
Muna taya murna da hare-haren makami mai linzami na Yaman da ke luguden makamai masu linzami a kan gidajen yahudawan sahyoniyawa safiya da dare.
Hare-haren makami mai linzami na Yaman mai albarka, wanda misali na baya-bayan nan shi ne harin makami mai linzami da aka kai a filin jirgin sama na Ben Gurion da safiyar yau, ya dagula barcin sahyoniyawan tare da ruguza tunanin tsaron karya na mai aikata laifin yaki Netanyahu da gwamnatinsa mai tsatsauran ra'ayi ke kokarin nunawa.
Ci gaba da kai hare-hare da makami mai linzami kan kasar Yamen yana tabbatar da fatattakar wuce gona da iri da Amurka ta ke yi kan kasar Yamen madaukakiya, da kuma tabbatar da cewa al'ummar kasar Yemen da gwamnati da kuma jagoranci al'ummar kasar 'yan uwa ne, masu aminci, masu gaskiya, masu goyon bayan al'ummar Palastinu, wadanda ke tunkarar yakin barnar sahyoniya da Amurka da a idon al'ummar duniya masu riya da munafukai baki daya.
Hamas ta yaba da hare-haren Ansarullah da sojojin Yemen
Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta fitar da sanarwa da ke cewa: Muna matukar godiya da irin gagarumin hare-haren da 'yan'uwanmu na Ansarullah da sojojin Yaman suka kai a cikin yankunan da suke karkashin gwamnatin sahyoniyawa.
Harin makami mai linzami da sojojin Yamen suka kai kan filin tashi da saukar jiragen sama na Ben Gurion da ke tsakiyar birnin Tel Aviv, ya nuna irin jajircewar da Yamen take yi a kullum kan al'ummar Palastinu, da kuma akidar ta ta hakika na tsayawa tare da al'ummar Palastinu da ake zalunta, duk kuwa da irin zaluncin da Amurka da sahyoniyawa suke ci gaba da yi kan kasar 'yan uwanmu.
Muna jinjinawa kasar Yemen, al'ummarta da kuma jagorancinta bisa asasi na jajircewarsu, da kuma ci gaba da bin tafarkin goyon baya da taimakon al'ummar Palastinu a zirin Gaza, wadanda ke fuskantar kisan kiyashi, muna kuma bayyana cikakken goyon bayanmu ga wannan kasa wajen tinkarar zaluncin Amurka da sahyoniyawan danniya.
Muna kira ga dukkan bangarorin al'ummar mu larabawa da musulmi da su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na tarihi na tallafawa Palastinu da kare al'ummarmu da ke fuskantar kisan kare dangi da yunwa a zirin Gaza. Muna kuma kira gare su da su shiga yakin kare alfarmar al'umma da tunkarar shirye-shiryen 'yan mamaya na fasikanci masu neman mamaye yankin da mallake albarkatun al'ummarsa.
Your Comment