Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa Ahlul Bayt (as) - ABNA - ya habarta cewa: a cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fitar ta bayyana cewa, maimaita zarge-zargen da ba su da tushe balle makama, ana mai alakanta ayyukan jaruntaka da al'ummar kasar Yemen suke yi wajen kare kansu da kuma goyon bayan al'ummar Palastinu ga kasar Iran a matsayin cin fuska ga wannan al'umma da ake zalunta.
Yana da kyau a san cewa sojojin Amurka su ne suka shiga yaki da al'ummar kasar Yamen domin nuna goyon bayansu ga kisan kiyashin da yahudawan sahyoniya suke aikatawa, inda suka aikata laifukan yaki ta hanyar kai hare-hare kan ababen more rayuwa da fararen hula a garuruwa daban-daban na kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa: Ko shakka babu goyon bayan da al'ummar kasar Yamen suke yi wa al'ummar Palastinu wani mataki ne mai cin gashin kansa da ya samo asali daga fahimtar da suke da shi na hadin kan bil'adama da Musulunci da 'yan uwansu na Palastinu, alakanta wadannan ayyuka ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran, da'awar batanci ne da bata da nufin boye laifukan da yahudawan sahyoniyawan suka mamaye yankunan Palastinu, da kara haifar da rugujewar yankin Palastinawa, da kuma haifar da rudani ga yankin Asiya.
Bayanin ya ci gaba da cewa: Ma'aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran bisa la'akari da matsayinta na wajabcin mutunta 'yancin kai da kuma yankunan kasa, ta tabbatar da yin Allah wadai da hare-haren da sojojin Amurka da suke kaiwa kan kasar Yemen, tare da la'akari da hakan a matsayin babban cin zarafi ga kundin tsarin mulkin MDD da kuma muhimman dokokin kasa da kasa.
A cikin wannan yanayi, ma'aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana babban sakamako da kuma tasirin ci gaba da wadannan hare-hare kan tsaro da zaman lafiyar yankin yammacin Asiya da na tekun Bahrul Ahmar, tana mai jaddada cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta dade tana yin kira da a kawo karshen kisan kiyashi da ake yi a Palastinu da aka mamaye, kasancewar su ne babban dalilin ci gaba da tabarbarewar yankin.
Daga karshe bayanin ya ci gaba da cewa: A yayin da Jamhuriyar Musulunci ta Iran take tabbatar da tsayuwar daka wajen kare kansu daga duk wani mataki na gaba da zai fuskanci kasar Iran, tana yin Allah wadai da irin barazanar da Amurka da yahudawan sahyoniya suka yi a baya-bayan nan kan kasarmu ta, tare da daukar nauyin gwamnatin Amurka da kungiyar 'yan ta'addar sahyoniyawan da ke da alhakin hakan da sakamakon da hakan zai iya haifarwa.
Your Comment