Ali Fayyad, memba na kungiyar Hizbullah a majalisar dokokin Lebanon yace: Babban abin da ya kamata a sa a gaba shi ne makiya Isra'ila su janye daga kasarmu, su daina kashe-kashen da suke yi a kullum, su daina kai hari kan fararen hula a kauyukan da ke kan iyaka don hana su komawa kauyukansu, da kuma kokarin fara aikin sake gina kasar cikin gaggawa, ba tare da wani sharadi ko wadansu alkwuran da ba za'a aikata su ba.
Dole ne gwamnati ta dauki matakin ko da kuwa da karancin albarkatunta, da dukkan karfinta, ta kuma mai da martani ga tattaunawar da tsokacin, ba tare da tabuka komai ba a nan da can.
Wannan aikin gwamnati ne kuma hakki ne na jama'a, kuma wannan aikin yana gaba da duk wani lissafin siyasa.
Wannan bayani na sa ya biyo bayan bayanin Shugaban Lebanon inda ya ce: An yanke shawarar takaita makamai ga sojoji!
A cikin sabon jawabin nasa, shugaban kasar Labanon Joseph Aoun ya ce, takaita makamai ga gwamnatin kasar, wani mataki ne da aka riga aka dauka.
Ya fadi wannan maganar ne yayin da masu wakiltar bangaren gwagwarmaya a majalisar dokokin Lebanon suka yi kakkausar suka ga wannan matakin.
Your Comment