Ranar Asabar 28 ga Shawwal 1446 (26/4/2026) aka kaddamar da littafin tarihin Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky, wanda ya bayar da kansa mai suna “RAYUWATA”.
A yayin jawabinsa a wajen taron, Shaikh Ibraheem Zakzaky ya bayyana cewa: “Na fadi wani abu a takaice (a gabatarwan littafin), cewa, wannan littafi sakamako ne na tunani da ya zo mana da muke tsare bayan waki’ar da aka sanya ma suna waki’ar Buhari, sai muka ga Allah Ta’ala ya bar mu da rai, tunda sun zo kisa ne kawai, ba yadda za a ce ma an rayu a wannan hali, amma dai da yake Allah ne me raya wa. Kamar yadda nace, Allah da ya kai Musa (AS) hannun Fir’auna, ya raine shi, sai ya kai mu hannunsu kuma, suna so su kashe amma kuma sai suna kula da mu.
Jagora ya ce: “Sai muka ga to tunda dama ta samu, bari mu fadi wani abu wanda watakila in ba mu muka fada ba ba za a sani ba. Ita Malama sai ta yi rubutu; ita ta rubuta ne, ta saka da Ingilishi ‘A brief history of the Islamic movement.’ Ni kuma sai na yi bayani da baki, ina fada tana sajjalawa, muna yi kamar muna magana ne, kamar ma tana min tambayoyi ne ina amsawa, sai dai da aka rubuta littafin ba a sa tambaoyin nata ba, sai aka mai da shi littafi. Amma kamar muna magana ne, idan mutum ya saurari sautin zai ji muna magana ne”.
Ya kara da cewa: “Kusan duk abin da na fada duk a takaice ne kuma a gurguje, domin kowane bangare na rayuwar zai zama akwai magana mai tsawo wanda shi kansa zai iya zama littafi. Alal misali, da zan ce zan bayar da labarin karatuna na zaure ne kawai, to ai zan yi littafi ne, amma kawai sai na fada a gurguje kawai. Haka karatun nizamiyya, shima zai iya zama littafi, amma shima sai ya tafi a gurguje. Kuma gidajen yari kowanne littafi ne”.
Shaikh Zakzaky ya yi tsokaci akan wasu daga kusa-kuran da aka samu daga aikin rubuta littafin daga ‘audio’ din bayanan, kamar amfani da kalmar ‘na yi’ maimakon ‘in yi’, da kuma yadda aka rubuta sunayen wasu mutane ba daidai ba, wanda ya yi fatan za a gyara kafin a sake bugawa.
Jagora ya yi bitan wasu daga abubuwan da ya kawo a cikin littafin da suka shafi rayuwarsa da darussan da za a dauka. Haka kuma ya kawo wasu daga darussan da ya bayar dangane da fitintinun da suka rika aukuwa a cikin Harka sakamakon kutsen makiya, inda ya ba da misalin wani rikici da ya riska bayan ya fito daga kurkukun Fatakwal karo na farko a tsakanin sistoci, da yadda ya warware shi. Da fitinar ‘yan Zuhudu da ita makiya suka kurdo da ita, da fitinar Tawayiyya”.
Yace, “Makiya ba sun daina ba ne, an dinga kunno fitina kenan, in sun yi na waje, sai su yi na ciki. Da yake wadansu abubuwan duk sun dan fiffito a labarinmu na Tajriba da muke samu, har takai ma a wani lokaci da nake bayani nake cewa, yanzu duk wata fitina da za ta kunno kai, ana farata mun santa sarai. Mutum ko guna-guni ya fara yi, mukan ce ahan, dama an taba yi; Faqad madat sunnatil auwalin. An riga an yi irinsa”.
Sakamakon raba taron da aka yi kashi biyu; na safe da na yamma, a kowanne Jagora (H) ya samu fitowa ya gabatar da takaitaccen jawabi, inda a karshe ya yi wa ‘yan uwa nasiha akan yin abu don Allah. Yace: “Ko tagwaye ne ake rigima, sai ka ji guna-guni ana cewa Ummah ta fi son Hassan, ko ta fi son Husaini, dubi yadda take ji da shi. To haka nan abin ya gada, a yi ta guna-gunin, amma in ka sa kanka kana yin abinka don Allah ne, kar ka damu da komai, a haka nan nasara za ta zo".
Ya kammala da cewa: “Amma in kace wai sai an kawar da duk matsaloli komai ya zama daidai, kowa ya zama ‘perfect’ to ai ba zai yiwu ba, kana neman ‘impossible’ ne, za ka bata lokacinka ne, a cigaba kawai haka nan, a yi ta yi kawai har a yi nasara insha Allah”.
Kafin jawabin Jagora (H), sai da aka gabatar da Dr. Hussaini Hassan, wanda ya yi sharhin littafin. Bayan tsokacin Jagora (H), an kira daidaikun ‘yan uwa da lajanonin Harka Islamiyyah, inda suka sayi kwafin littafan. A cikin mako mai kamawa za a cigaba da kaddamar da littafin a Da’irorin kasar nan kamar yadda kwamitin kaddamarwar suka ba da sanarwa.
Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)
26/04/2025



































Your Comment