24 Afirilu 2025 - 18:34
Source: ABNA24
Ansarullah: Wajibi Ne Ga Al'ummar Musulmi Su Tanadi Ƙarfin Kare Kansu

Jagoran Ansarullah na kasar Yaman: Makiya yahudawan sahyoniya a Gaza ba su iya katabus na soji ba, don haka suka koma yin karya.

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As -Abna- ya habarta cewa: Sayyid Abdul Malik Badreddin al-Houthi: Kisan kare dangi, komai yawansa, ba a daukar a matsayin nasarar soja.

Ya fito fili karara cewa batun fursunonin ba ta da wani muhimmanci ga mai laifin ta'addanci Netanyahu da kungiyarsa.

Ainihin manufar makiya ita ce al'ummar Palastinu suyi kaura daga zirin Gaza. Makiya sun karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kuma musayar fursunoni a baya tare da kwarin gwiwar Amurka, bayan da Amurka ta fito fili kuma karara ta sanya batun korar al'ummar Gaza cikin ajandarta.

Samun karfin hana ruwa gudu ya zama wajibi ga al'ummar musulmi. Samun iko don kare kai da kuma kokarin tabbatar da karfi da kiyaye tsarin mulki wani lamari ne da ya wajaba ga al'ummar musulmi baki daya.

An kai wa al'ummar Palasdinu hari ta kowace fuska kuma suna bukatar karin karfi da makamai.

Akwai gagarumin kokari da yahudawan sahyoniya da 'yan amshin shatansu suke yi na kaddamar da yakin ruwan sanyi don nufatar dukkanin al'ummar musulmi.

Kafofin yada labaran Isra'ila suna yin alfahari da goyon bayan sojojin Amurka tare da jaddada cewa manyan makamai na kan hanya daga Amurka.

Your Comment

You are replying to: .
captcha