Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As -Abna- ya habarta cewa: Bisa cewar fadar Vatican, Paparoma Francis shugaban mabiya darikar Katolika na duniya ya rasu yana da shekaru 88 a duniya bayan fama da rashin lafiya.
Paparoma Francis, shugaban mabiya darikar Katolika na duniya, wanda ya jima yana jinya kuma yana samun sauki kamar yadda fadar Vatican ta bayyana, ya rasu a yau litinin.
An haifi Paparoma Francis a ranar 17 ga Disamba, 1936, a Argentina, mai suna Jorge Mario Bergoglio. Ya karbi matsayin Cardinal daga Paparoma John Paul II a shekara ta 2001. An zabi Bergoglio Paparoma a shekarar 2013, ya maye gurbin Benedict na 16, kuma ya dauki lakabin Francis. Shi ne memba na farko na tsarin Jesuit, Paparoma na farko daga Amurka, kuma, bayan Gregory III, Paparoma na farko wanda ba na Turai ba.
Your Comment