25 Faburairu 2025 - 20:39
Duk Lokacin Da Mutum Ya Kasance A Cikin Masallaci Ana Rubuta Masa Laɗan Yin Ibada Ne

Wannan bayani wani ɓangare ne daga cikin hudubar sallar Juma'a ta wannan makon a birnin Aalishahr Bushehr Iran, ranar 22 ga watan Fabrairu 2025, wanda Sheikh Hujjatul Islam Walmuslimin Hamidinejad, babban limamin Juma'a na birnin ya gabatar.

Wannan bayani wani ɓangare ne daga cikin hudubar sallar Juma'a ta wannan makon a birnin Aalishahr Bushehr Iran, ranar 22 ga watan Fabrairu 2025, wanda Sheikh Hujjatul Islam Walmuslimin Hamidinejad, babban limamin Juma'a na birnin ya gabatar.

Inda ya fara godiya ga Allah Ta'ala tare da salati ga Annabin Rahama da iyalansa tsarkaka ya dora da cewa: "Kwanaki goma na karshe na watan Sha'aban suna a matsayin kwanaki goma na girmama masallatai da karkaɗe kurar masallatai, saboda wannan dalili, zan so in yi bayanin wasu abubuwa game da masallaci. Masallaci shine zuciya a cikin al'ummar musulmi, kuma shi ne mafi muhimmanci cibiyar al'adu da siyasa na gwamnatin addini. Allah Ta'ala A cikin ayoyi da ruwayoyi ya kebanci masallaci da matsayi mai girma inda ya kira su da Ɗakunansa. 

Annabi (SAW) ya ce dakunan Allah a bayan kasa sune masallatai, kuma Allah yana girmama duk wanda ya ziyarce shi a cikin masallatai, aya ta 18 cikin Surar Jin, yana cewa:" masallatai na Allah ne...".

Manzon Allah (S.A.W) ya ce a wata ruwayar cewa zuwa masallaci yana kawo rahamar Allah ga mutum, kuma wanda da gangan bai zuwa masallaci, zai zama munafuki, kuma idan wata musiba ko cuta ta sauka, wadanda ke kusantar masallacin za su samu kariya, haka nan a cikin Suratul Taubah aya ta 18, tana cewa: "Waɗanda suke raya masallaci ɗakunan Allah da halartar su cikinsa sune Muminan wadanda suka yi imani da Allah da ranar lahira suke yin Sallah suke bada Zakka kuma ba sa tsoron kowa sai Allah Ta'ala. Kuma Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam) ya ce: “a ranar alkiyama Allah Ta'ala zai ce "Ina maqwabtana?” Sai Mala’iku su ce: “wane ne ya cancanta ya zama makwabcinka?” sai Allah Ta'ala ya ce: " Sune waɗanda suke raya masallaci.

Halartar masallaci ba wai kawai ya takaita ne lokacin sallah kawai ba ne, sai dai ya zamo ne duk lokacin da mutum ya kasance a cikin masallaci ana rubuta masa ladan yin ibada ne, ko da kuwa bai yi wata ibada ba, Manzon Allah (SAW) ya ce, “Matukar kana cikin masallaci, duk numfashin da za ka yi, za'a daga darajar matakinka zuwa sama a cikin Aljanna, kuma Mala’iku za su yi salati a gare ka, kuma za a rubuto maka ayyukan alheri guda goma.

Idan aka yi sakaci da masallaci zai koka ranar kiyama, akwai wani hadisi daga Imam Sadik (AS) yana cewa masallatai za su kai kara ga Allah a ranar kiyama game da makwabtansu da ba su halarci masallaci ba, sai Allah Ya ce musu: “ na rantse da girmana da daukakata, ba zan karbi ko da Sallah daya ce daga gare shi ba, kuma ba zan yi masa rahama ba.

A yau da makiya Musulunci suka fuskanci mummunan shankaye daga masallatai, suna kokarin hana matasa da samari zuwa masallatai, don haka dole ne mu yi kokarin jawo hankalin matasa da samari domin su rinka zuwa masallaci...